BH: An kai wa tawagar hafsan sojoji hari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kai harin ne akan 'yan tawagar gaba na babban hafsan sojin

A ranar Asabar ne wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar, Tukur Burutai hari a kauyen Faljari da ke tsakanin Mafa da Dikwa.

wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin, Kanar Sani Usman-Kuka-sheka, ta ce an kai harin ne akan wasu daga cikin sojojin da ke tawagar hafsan wadanda suka wuce gaba.

Sai dai kuma sanarwar, tace maharan ba su ji da dadi ba a hannun sojojin a inda sojojin suka kashe 'yan kungiyar har mutum 10, suka kuma kama guda 5 a raye.

Sanarwar ta kara da cewa soja daya ya rasa ransa a lokacin gumurzun sannan wasu guda 4 sun jikkata.

A a ranar Asabar din ne hafsan sojojin Laftanar Janar, Tukur Burutai ya ziyarci sansanonin rundunonin sojin da ke yaki da Boko Haram wadanda ke a garuruwan Mafa da Dikwa da logomani.

A lokacin ziyarar dai, hafsan sojojin ya yaba wa sajojin bisa irin namijin kokarin da suke yi wajen kakkabe boko haram daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Harwayau, laftanar janar Burutai ya gana da taron 'yan gudun hijra a garin Dikwa a inda ya shaida musu cewa su kwantar da hankalinsu ba bu wani abu da zai same su.