Birtaniya ta sake bude ofishin jakadancinta a Iran

Ofishin jadakancin Biritaniya a Iran Hakkin mallakar hoto AP

Birtaniya ta sake bude ofishin jakadancinta da ke Iran a matakin baya-bayan nan na kyautata dangantaka tsakanin Iran da kasashen yamma.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Philip Hammond, ya albarkaci bikin, inda aka kafa tutar Birtaniya a karon farko cikin shekaru hudu.

Mista Hammond ya ce sake bude ofishin jakadancin shi ne matakin azanci na gaba bayan yarjejeniyar da aka cimma a kan shirin nukiliyar Iran din a watan da ya gabata.

Sai dai ya shaidawa BBC cewa har yanzu akwai batutuwa, wadanda Iran da Birtaniya suke da sabani amma a shirye suke su tattauna a kan su.

Ya ce, "A akwai bukatar mu fara a hankali, kuma cikin nutsuwa, domin gina sabuwar dangantaka sannan mu ga yadda tafiyar za ta kasance."