Birtaniya za ta sake bude ofishin jakadancin ta a Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Philip Hammond

Ministan harkokin kasashen wajen Birtaniya, Philip Hammond zai je kasar Iran domin sake bude ofishin jakadancin Birtaniya a Iran shekaru 4 bayan rufe shi biyo bayan harin da wasu masu zanga-zanga a kasar suka kai wa ofishin.

Kazalika ita ma Iran za ta bude nata ofishin jakadancin a Birtaniyyar duk a yau Lahadi inda jakadan ta a Birtaniya Ajay Sharma da kuma wasu wakilai daga ma'aikatar harkokin wajen Iran din za su yi.

Ziyarar Mr Hammond zuwa Iran manuniyace cewa kasashen biyu za su cigaba da kulla dangantaka bayan Iran din ta sanya hannu akan yarjejeniyar shirinta na makamashin nukiliya.

Mista Philip zai samu rakiyar tawagar 'yan kasuwar Birtaniya abin da ke nuna akwai yiwuwar tattaunawa kan batun cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Wannan kuma ita ce ziyarar wani jami'in birtaniya zuwa Iran din ta farko a tsawon shekaru 12.