An gano wasu kaburbura a Mayalysia

'Yan sandan Malaysia sun ce sun gano wasu gawarwaki da dama da aka binne kusa kan iyakar kasar da Thailand, a wani yanki da masu safarar mutane suke bi.

An gano gawarwaki ashirin da hudu a kusa da inda aka gano wasu gawarwakin mutane fiye da dari daya a watan Mayu.

Ana kyautata tsammanin mutanen musulmi ne yan Rohingya wadanda ke gujewa azabtarwa a Myanmar da kuma yan Bangladesh wadanda ke neman kyautatuwar rayuwar a kasashen waje.

Bayanan hoto,

Ana kyautata zaton gawawwakin na 'yan kabilar Rohinga ne na Myanmar.

Masu aiko da rahotanni sun ce akwai yiwuwar gawarwakin da aka gano na baya bayan ya sake ta do da muhawara a game da ko Malaysia tana yi wani kokari na hana safarar mutane.