'Yan cirani sun shiga Macedonia

'Yan cirani a iyakar Macedonia
Image caption 'Yan ciranin na cike da fatan isa nahiyar turai dan samun kyakkyawar rayuwa.

Daruruwan yan gudun hijira daga Syria suna a kwarara cikin Macedonia bayan da hukumomi suka bude iyakar kasar da Girka.

'Yan gudun hijirar suna hawa jiragen kasa da kuma motocin safa zuwa Serbia inda suke fatan shiga kasar Hungary daga nan kuma su shiga wasu kasashen arewacin Turai.

A ranar alhamis da ta wuce kasar ta Macedonia ta ayyana dokar ta baci inda ta rufe iyakar ta kudanci, inda yan sanda suka harba gurnetin dimautawa da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa cincirindon yan ciranin.

Yan gudun hijira kimanin dubu biyu ne ke isa kasar Hungary a kowace rana gabanin kamalla aikin shingen waya domin hana su wucewa.