Kamfanin Spotify ya bada hakuri

Shugaban kamfanin Spotify Daniel Ek ya ba da hakuri akan fushin da mutane suka nuna akan sabon tsarin da ya fitar game da wakokin da ya samar wa masu amfani da shafinsa.

Wasu masu amfani da shafin sun ce zasu dai na amfani da shi saboda wasu sharudan da ya fitar da kuma sauye sauyen da ya yi.

Wasu daga cikin sharudan sun hada da yadda mutum zai iya samun hotanni da lambobi wayoyi da kuma bayanan da ke cikin wayar komai da ruwanka.

Mr Ek a cikin shafinsa na internet ya bada hakuri akan rudani da sauye sauyen suka janyo.

Ya kuma yi alkawarin inganta sabon tsarin sai dai be yi magana kan ko za'a sauya sabbin kaidojin ba.

"Ya kamata a ce mun yi aiki da ya fi wannan inganci wajenm sanar da mutane wadannan tsare tsare".

Haka kuma ya ce kamfanin ba zai amfani da hotuna ko lambobi ko bayanan GPS na mutane ba tare da amincewarsu ba.