An sako dan Birtaniya daga Yemen

David Cameron Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An sako dan Burtaniyar ne bayan da hadaddiyar daular larabawa ta shiga batun.

An sako wani dan Birtaniya da akai garkuwa da shi a kasar Yemen, bayan shiga lamarin da sojoji suka yi da hadaddiyar daular labara.

A wata sanarwa da ofishin harkokin wajen kasar ya fitar, an bayyana cewa mutumin da ba a bayyana sunansa ba ya na cikin koshin lafiya, ya na kuma karbar taimako.

Kamfanin dillancin labaran hadaddiyar daular larabawa ya wallafa cewa mayaakn kungiyar al-Qaeda ne sukai garkuwa da mutumin, amma a yanzu an dauke shi zuwa birnin Abu Dhabi a jirgin saman Sojin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa yarima mai jiran gadon hadaddiyar daular larabawa yana tattaunawa Firayinmistan Birtaniya David Cameron kan batun sako mutumin.