An samu raguwa a hayakin da ke gurbata muhali

An samu raguwa a yawan hayaki mai gurbata muhali da ake fitarwa a yankin gabas ta tsakiya ya yinda ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a kasar Syria.

Tashe tashen hankula da ake fuskanta a yankin gabas ta tsakiya tun daga shekara ta 2010 sun sa an samu raguwa a yawan hayaki da ake fitarwa da ke gurbata muhali.

Masu bincike sun ce a kasashe irinsu Syria da Iraki an samu matukar raguwa a yawan hayaki da ke gurbata muhali.

Yawan hayaki da ake fitarwa da ke dauke da sinadarin nitrogen dioxide a birnin Damascus ya ragu da kashi hamsin cikin dari tun bayan da aka soma yakin basasa a kasar ta Syria.

Sai dai a kasar Lebanon an samu karuwa ne a yawan hayaki da ke gurbata muhali da kashi talatin cikin dari saboda yawan yan gudun hijira dake kwararowa cikin kasar.

Sai dai rahoton ya ce tasirin da mayakan kungiyar IS da ke ikirarin jihadi suke yi a arewa maso yammacin Bagadaza na kasar Iraki ya sa an samu raguwa a yawan hayaki da ke gurbata muhali da ake fitarwa.

Mawallafan rahoton sun yi ammanar cewa akwai darusan da za'a koya game da aikinsu a kan yawan hayakin mai gurbata muhali da kasashen duniya ke fitarwa.