Za a yi bincike a kan sayen makamai a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anazargin tafka cuwa-cuwa wajen sayo kayan yakin sojin Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci mai ba shi shawara a kan tsaro ya nada kwamitin da zai yi bincike kan yadda aka sayo makaman da sojin kasar ke amfani da su tun daga shekarar 2007 zuwa yanzu.

Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban ya ce kwamitin zai yi bincike ne a kan matsalolin da aka fuskanta wajen sayo makaman da kuma cuwa-cuwar da ke cikin sayo su.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasar ya dauki matakin ne domin magance matsalar cin hanci da ake samu a ma'aikatan gwamnati.

A kan haka ne mai bai wa shugaban shawara a kan tsaro ya nada kwamiti mai goma sha uku a karkashin jagorancin AVM J.O.N. Ode mai ritaya.

Sauran mambobin kwamitin su ne: R/Adm J.A. Aikhomu, mai ritaya da R/Adm E. Ogbor da Bigediya Janar L. Adekagun (rtd.),Birgediya Janar M. Aminun-Kano (rtd.) da Birgediya Janar N. Rimtip (rtd.) da Cdre T.D. Ikoli da Air Cdre U. Mohammed (rtd.) da Air Cdre I. Shafi'i da Col A.A. Ariyibi da Gp Capt C.A. Oriaku (rtd.) da Mr. I. Magu (EFCC) da Birgediya Janar Y.I. Shalangwa, a matsayin Sakatare.