Kaduna: An gano makarantun bogi 33

Image caption Malam Nasir El Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta gano wasu makarantun firamare 33 na bogi.

An gano makarantun ne a ci gaba da aikin tantance ma'aikata da gwamnatin jihar ta gudanar.

Wata majiya ta ce, makarantun da aka gano na bogi suna da ma'aikata na kowanne …ďangare da ake biya albashi, amma a zahiri babu makaratun.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, tana kokarin tantance ma'aikata domin kawo karshen almundahana da sunan biyan albashi.

Aikin tantace ma'aikatan, ya zuwa, yanzu ya ceto naira miliyan 120 a watan Agusta, inji gwamnatin jihar Kaduna.

Gwamna Nasir El Rufai ya ce, aikin tatancewar zai tsaftace kundin biyan albashi na jihar.