Hannayen jari sun sake faduwa a China

Kasuwar hada hadar hannayen jari ta China Hakkin mallakar hoto XINHUA
Image caption Kasuwar hada hadar hannayen jari ta China

Kasuwar hada-hadar hannayen jari a China ta sake faduwa da fiye da kashi shida cikin dari kafin daga bisani ta farfado kadan.

Hakan ya biyo bayan faduwar fiye da kashi takwas da digo biyar cikin dari a jiya Litini, wanda shi ne mafi girma da China ta taba fuskanta tun shekarar 2007.

Rahotanni sun ce a sauran wurare na yankin Asiya, kasuwar hannayen jarin na ci gaba da tangal-tangal.

Wannan dai ya biyo bayan fargabar da masu saka jari ke ci gaba da nunawa ne akan tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin China ke yi.