'Yan siyasar Nijar na kulla kawance

Image caption Dan siyasa Niger Hamma Amadou

A Jamhuriyar Nijar, wasu tsofaffin na hannun daman Hamma Amadou sun kafa wata jam'iyar siyasa a shirye shiryen da ake yi na zabuka kasar a shekara mai zuwa.

Jam'iyar mai suna AMEN a takaice ta ce za ta bayar da gudummuwa wajen bunkasa demokaradiya, habaka tattalin arziki, da kyautata jin dadin rayuwar 'yan Nijar.

Wasu fitattun 'Yan siyasar a Nijar din ne dai suka kafa sabuwar jam'iyyar.

An dai kafa wannan sabuwar jam'iyyar a dai dai lokacin da wasu 'yan adawan kasar na gungun ARDR tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin farar hula suka kafa wani sabon kawance mai suna FPR a takaice.