Nigeria: Za a kafa kamfanin jirgin sama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Muhammadu Buhari, shugaban Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin a farfado da kamfanin jiragen sama na kasa domin samar da ayukan yi da dawo da martabar kasar.

Sanarwa daga ma'aikatar zirga-zirgar jiragen sama tace, an kafa kwamiti da zai duba ko me yasa kamfanin Nigeria Airways da ma wasu kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu suka durkushe.

Kwamitin zai tattauna da bangarori daban-daban da suka hada da kamfanonin kasashen waje domin kafa kamfanin jiragen sama na Najeriya da hadin gwiwar 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Najeriya ba ta da kamfanin jiragen sama na kasa tun daga shekara ta 2003 bayan durkushewar Nigeria Airways.

Koda sauran kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu suna cikin wani hali da suka hada da bashi mai yawa.