Ana ha'inci da sunan tallafin mai - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi gwamnatocin ƙasar da suka shude da saka kasar cikin mawuyacin hali sakamokon ha'incin da suka yi wajen kashe biliyoyin Nairori kowacce shekara da sunan biyan tallafin shigo da mai.

Shugaban ya yi wannan kalamin a Abuja a yayin ganawarsu da shugaba da kuma 'yan majalisar gudanarwar Hukumar tattarawa da rarraba arzikin kasa.

A cewar shugaba Buhari yadda kudaden tallafin mai suka riƙa hauhawa cikin 'yan shekarun nan wata hanya ce da ta bude kofar lalacewar matatun mai na kasar.

Shugaba Buhari ya nuna matukar bacin ransa dangane da yadda aka bar matatun man Najeriya suka tabarbare.

Batun tallafin mai dai yana cike da badaƙalar cin hanci da rashawa.