An hallaka mutane 20 a rikicin CAR

Hakkin mallakar hoto PACOME PABANDJIAFP
Image caption Jami'an tsaro ne suka kwantar da kurar rikicin

Mutane a kalla 20 ne aka hallaka a cikin kwanakin da aka shafe ana gwabza rikicin addini a kasar Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

An kuma jikkata wasu karin mutane 15.

Tashin hankalin a yankin Bambari ya fara ne ranar Alhamis, lokacin da wasu masu gwagwarmaya da makamai kiristoci suka hallaka wani matashi Musulmi.

Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta shiga cikin lamarin.

Dubannin mutane ne suka mutu a rikicin addinin Jamhuriyar Tsakiyar Afirkar, da juyin mulkin shekara ta 2013 ya tunzura.