Mutane 5 sun mutu a harin Damaturu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ganau sun shaida wa BBC cewa wata mace ce ta kai harin.

Hukumomi a jihar Yobe da ke Najeriya sun ce mutane biyar ne suka mutu bayan harin kunar-bakin-wake da aka kai tashar mota a Damaturu ranar Talata.

A wata sanarwa, kakakin gwamnatin jihar Abdullahi Bego ya ce fiye da mutane 20 suka jikkata sakamakon harin.

Ya kara da cewa an kai mutanen da suka jikkata zuwa asibiti inda ma'aikatan gaggawa ke kula da su.

Kazalika, ya ce jami'an tsaro sun kewaye wurin da aka kai harin.

Ganau sun shaida wa BBC cewa wata mace ce ta kai harin.