Ana korafi akan alkalamin Samsung Galaxy

Wayar komai da ruwanka na Samsung Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wayar komai da ruwanka na Samsung

Alkalami na musaman na wayar komai da ruwanka na kamfanin Samsung watau Note 5 stylus na kawo damuwa ga wasu dake amfani da wayar.

Wasu da suka soma amfani da sabuwar wayar ta samsung sun ce akwai matsala a kan yadda aka tsara alkalamin.

Za'a dai iya saka alkalamin a jikin wayar ta komai da ruwanka sai dai idan aka saka shi ba dai dai, toh hakan kan lalaa alkalamin ko ya sa wayar ta lalace idan aka yi amfani da karfi wajen cire alkalamin.

Sai dai kamfanin Samsung ya yi kira ga masu amfani da wayar akan su bi kaidojin amfanin da wayar kamar yadda a tsara a cikin takardar bayani akan yadda za'a sarafa wayar.

A yanzu dai a kasashen Amurka da kasashen Asiya ake samun wayar.

Sai dai wasu sun nuna damuwa akan cewa za'a iya fuskantar matsala makamancin wannan idan aka kaddamar da wayar a kasashen Turai