Ghana ta turo 'yan sanda Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Chris Stein AFP
Image caption An zabi 'yan sandan ne daga wata rundunan 'yan sanda ta musamman

A kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, kasar Ghana ta tura 'yan sanda dari da saba'in ciki har da wasu manyan hafsoshin 'yan sandan da suka hada da likitoci.

An dai zabi 'yan sandan ne daga wata rundunan 'yan sanda ta musamman wadda ta kware wajen kwantar da tarzoma da kuma amfani da karfi dai-dai kima wajen ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Ana sa ran 'yan sandan za su taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu da ke fama da rikice-rikice.

Rahotanni sun ce za a fara tattaunawa a Majalisar Dinkin Duniya kan batun sanya takunkumi ga duk wasu da ke yin zagon kasa ga batun samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.