Assad- Ina da karfin gwiwa a kan Rasha da Iran

Bashar Al Assad Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bashar Al Assad

Shugaban kasar Syria, Bashar al Assad, ya ce ya na da karfin gwiwar cewa Rasha da kuma Iran zasu mara masa baya.

Mr Assad ya yi watsi da jita jitar da wasu ke yi a kan cewa watakila kasashen biyu su juya masa baya domin cimma matsaya a kan rikicin kasar ta Syria.

Hakan ya biyon bayan yarjejeniyar shirin nukliya da kasashen yamma suka cimma da kasar Iran a baya baya nan.

A hirar da ya yi da wata kafar talibijin ta kasar Lebanon Mr Assad ya soki mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya, Stefan de Mistura inda ya ce yana goyon bayan wani bangare.