Ashley Madison: Wasu sun kashe kansu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Toronto ba su yi karin bayani ba kan mutuwar mutanen.

Jami'an 'yan sanda a Canada sunce wa su mutane biyu da ke muamala da shafin sada zumunta ta ma'aurata dake soyayya a waje ta Ashley Madison sun kashe kan su.

'Yan sandan Toronto ba su yi karin bayani ba kan mutuwar mutanen.

An dai yi kutse ne a rumbun adana bayanai tare da sace bayanan sirrin na mutane fiye da miliyan talatin da uku a shafin da ke ba ma'abotar sa damar kulla dangantaka ta soyayya tsakanin su.

Kamfanin Avid Life Media da ke kula da shafin ya yi alkawarin bayar da kyautar dala dubu dari biyar ga duk wanda ya gabatar da bayanai da za su kaiga cafke mutanen da suka yi kutse a shafin.