An kama wasu mutane a kan hatsarin China

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Wajen da abubuwa suka fashe a China

'Yan sanda a China sun kama wasu mutane 12 wadanda ke aiki a kamfanin da yake da wajen ajiyar kayayyaki inda wasu manyan abubuwa suka fashe a wajen a farkon watan da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran kasar Xinhua ya ce daga cikin mutanen da aka kama sun hadar da shugaban kamfanin Yu Xuewei da mataimakinsa Dong Shexuan da kuma wasu mataimakn manajoji a kamfanin guda uku.

Ana dai zargin su da ajiye wasu sinadarai masu ila ba bisa ka'ida ba.

Masu shigar da karar suna kuma zargin wasu jami'ai a tashar ruwan da yiwa aiki rikon sakainar kashi lamarin da ya sa har aka shigo tare da ajiye sinadarai masu illa a Tianjin.

Kimanin mutane 139 ne dai suka rasa rayukansu sakamakon fashewar abubuwan yayin da da dama kuma suka jikkata.

Kazalika gine-gine da kuma motocin da ke kusa da wajen da abin ya faru duk sun kone.