Shugaba Salva Kiir ya mika wuya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana zaman dar-dar a Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya sanya hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tare da 'yan tawayen kasar.

Yarjejeniyar za ta share fagen kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da shugaban 'yan tawaye, Riek Machar.

Dama dai jagoran 'yan tawayen Riek Machar ya sa hannu a kan yarjejeniyar a makon da ya wuce.

Shugabannin kasashen yankin irinsu Uhuru Kenyatta na Kenya, da Yoweri Musaveni na Uganda, da kuma Hailemariam Desalegn na Ethiopia sun shaida sanya hannu a kan yarjejeniyar a birnin Juba na Sudan ta Kudu.

A shekara ta dubu biyu da sha daya ne, Sudan ta Kudu ta samu 'yan cin kai, amma ba da jimawa ba kasar ta auka cikin mummunan yakin basasa a shekara ta 2013.

Fada tsakanin magoya bayan bangarorin biyu ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallinsu.