Ana bikin #RanarHausa a Twitter

Image caption Hausawa da dama suna amfani da shafukan sada zumunta na zamani.

Masu mu'amala da shafukan sada zumunta na zamani a Najeriya suna bikin #RanarHausa, musamman a shafin Twitter.

Mutumin da ya kirkiri maudi'in, Abdulbaqi Aliyu, ya shaida wa BBC cewa sun ware ranar 26 ga watan Agusta ne domin nuna wa duniya irin tasirin da harshen Hausa ke da shi.

Ya kara da cewa yawanci Hausawan wannan zamani ba su cika kulawa da kuma yada harshensu ba, don haka wannan rana za ta tunatar da su.

Daruruwan masu amfani da Twitter ne suka rika wallafa jawabai kan muhimmancin da harshen hausa ke da shi.

Wannan shi ne karon farko da ake yin bikin na #RanarHausa.