Buhari ya yi sabbin nade-nade

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana jiran Buhari ya sanar da mukamai a gwamnatinsa

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade, da suka hada da na Sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Babachir David Lawal daga jihar Adamawa sai kuma Alhaji Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa.

Buhari ya nada Kanar Hameed Ibrahim Ali mai ritaya, a matsayin shugaban hukumar kwastam da kuma Mr. Kure Martin Abeshi a matsayin shugaban hukumar shige da fice.

Sabon babban mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin majalisa, a bangaren majalisar dattajai shi ne Sanata Ita S.J Enang, sai kuma Honorobul Suleiman A. Kawu a matsayin babban mai taimakawa shugaban kasa a bangaren majalisar wakilai.

Sanarwa da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ce mutanen za su kama aiki ne daga ranar 27 ga watan Agusta.