Dangote zai bude kamfanin siminta a Kamaru

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ya kafa babban kamfanin siminti a Kamaru.

Firayi Ministan Kamaru, Philemon Yang, zai kaddamar da babban kamfanin yin simintin da hamshakin attajirin nan na Najeriya Aliko Dangote ya kafa a cibiyar kasuwancin kasar watau Douala.

Najeriya ta zamo babbar kawar cinikayyar Kamaru, kuma kamfanin siminti na Dangote shi ne mafi yawan jari da aka sa a kasar.

A ranar Laraba ne kamfanin siminti na Dangote a Najeriya ya sanya hannu a kwangilar sama da dala biliyan hudu da miliyan dari uku, inda kamfanin zai gina kamfanonin simintin ne a kasashen Kamaru, Habasha, Kenya, Mali, Nepal, Niger, Senegal da kuma Zambia.

Tattalin arzikin Afrika ya fadi sosai a kasuwar hannun jari, amma akwai alamun zai farfado a fannin gine-gine, kuma da alama kasuwar siminti za ta bunkasa.