Turirin da na'urorin kan fitar na da illa ga lafiyar wasu mutane

Image caption Turiri

Wata Kotu tace a bawa wata mata diyya saboda turirin lantarki da wata na'ura ke fitarwa ya ja mata illa ga lafiyarta.

Matar mai suna Marine Richard 'yar kimanin shekaru 39 da haihuwa zata rinka karbar fam 580 a kowanne wata har tsawon shekaru uku.

Marine ta ce za a iya samun mutane da irin wannan lalura ta ta wanda turirin wata na'ura kan iya musu illa.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta yi nazari akan wannan lalura inda ta ce hakan na iya faruwa amma kuma har yanzu ba a kai ga gano abinda ke janyo hakan ba.

Ita dai wannan mata tana zaune ne a wani kauye wanda ke da tsaunuka a kudu maso yammacin kasar Faransa.

A inda ta ke zaunen babu wutar lantarki, ta kuma ce a kullum tana samun matsala daga turirin abubuwa da suka hadar da na wayoyin salula.

Rahotanni sun ce alamomin dake nuna cewa mutum nada irin wannan matsala irinta Marine sun hadar da ciwon kai da yawan gajiya da tashin zuciya da kuma haki.

Wata kotu ce dake zamanta a Toulouse ta bayar da umarnin na biyan wannan mata diyya akan lalurar dake damunta da ake kira EHS.

A kasar Amurka ma iyayen wani yaro dan kimanin shekaru 12 da haihuwa sun yanke shawarar shigar da kara saboda yaron su da yake karatu a wata makarantar kwana yana fama da makamanciyar wannan lalura inda na'urar WiFi dake a makarantar ke janyo masa lalurar.

Iyayen yaron sun ce an gano yana da wannan lalurar inda turirin wata na'ura ke haifar masa da matsala ga lafiyar sa.

Makarantar da yaron ke karatu ta bukaci wani kamfanin fasahar sadarwa da ya binciko abinda ke janyo kamuwa da wannan lalura.