Ba a ba mu tallafin kudi ba — gwamnoni

Gwamanonin jihohin Najeriya Hakkin mallakar hoto State House Twitter
Image caption Gwamanonin jihohin Najeriya

Gwamnonin jihohin Najeriya sun bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta bai wa jihohinsu tallafin da ta yi alkawarin ba su domin ceto su daga matsalar tattalin arziki da kuma dimbin bashin albashin ma'aikata ba.

Gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya shaida wa BBC cewa sun fahimci cewa kudin da za a ba su ba tallafi ba ne, bashi ne da gwamnatin tarayya ke bukatar su karba da sunan tallafi.

Ya kara da cewa suna kan kokarin karbar kudin daga wajen bankuna.

A kwanakin baya ne gwamnonin jihohin Nijeriya wadanda bashi ya yi wa katutu suka tunkari gwamnatin tarayya da kokon bara, domin ta ba su kudade su biya bashin albashin ma'aikata da suka gada daga gwamnonin da suka gabace su.