An hallaka kwamandojin sojin Iraki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar IS na tafka ta'asa a Iraki

An hallaka wasu manyan sojoji masu mukamin janar a kasar Iraki a wani harin kunar-bakin-wake da aka kai da wata mota makare da bama-bamai a kan hedikwatar rundunar sojin kasar da ke arewacin Ramadi.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.

A watan Mayun da ya wuce ne 'yan kungiyar IS suka kwace iko da Ramadi, lamarin da masu lura da al'amura ke cewa babban koma-baya ne ga gwamnatin Iraki.

Sojojin kasar sun yi yunkuri daban-daban da nufin kwace iko da Ramadi.

Kawo yanzu ba su cimma wata nasara sosai ba, kuma da wannan kisan da aka yi wa Kwamandojinsu, giwiwarsu ka iya sanyi.