Ana cin zarafin 'yan jarida a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ellen Johnson Sirleaf

Kungiyar 'yan jaridu a kasar Liberia ta yi kira ga 'yan sanda da su daina kawo barazana ga Mambobinta.

Kungiyar ta ce tana yawan samun korafe-korafe daga 'ya'yan ta na cewa ana dukan su tare da wulakanta su a lokuta da dama.

Mai rikon mukamin shugaban kungiyar Jallah Greyfield ya ce an wulakanta wani dan jarida sosai saboda kawai ya tambayi wani dan sanda tambayar da bata yi masa dadi ba.

A baya dai Kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya sun soki kasar Liberia saboda wulakanta aikin jarida.

Har yanzu dai 'yan sandan ba su ce komai ba game da wannan zargi da ake musu.