'Daruruwan 'yan ci-rani sun mutu a teku'

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan ci rani masu tafiya a jiragen ruwa

Daruruwan mutane ne ake fargabar sun mutu lokacin da wasu jiragen ruwa biyu dauke da kimanin mutane 500 suka kife a tekun Libya a kusa da birnin Zuwara.

Rahotanni sun ce ana can ana aikin ceto daya daga cikin jiragen biyu daya kife ranar Alhamis, yayin da jami'ai dake gadi a teku Libya suke ci gaba da laluben dayan jirgin.

Rahotannin sun nuna an kubutar da kimanin 'yan ci rani 20 da ke cikin jiragen.

Wata majiya a Zuwara ta shaida wa BBC cewa an kai gawarwakin kimanin mutane 100 wani asibiti da suka hada da na 'yan kasashen Syria da Bangladesh da wasu dake yamma da Sahara.

Dakarun dake gadin teku a Libya suna da karancin kayan aiki na gudanar da babban aikin ceto a teku.