NNPC ya soke kwangilar dakon danyen mai

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ana zargin aikata cin hanci da rashawa a NNPC

Kamfanin mai na Nigeria, NNPC ya soke kwangilar dakon danyen mai da jiragen ruwa zuwa matatun man kasar da ke Warri da Fatakwal da kuma Kaduna.

NNPC ya ce ya dauki matakin ne saboda an saba ka'ida wajen ba da kwangilar a baya, sannan kuma akwai matukar tsada a tsarin.

Sanarwa da kakakin NNPC, Ohi Alegbe ya fitar ta ce an soma gudanar da wani sahihin tsari domin ba da wannan kwangilar ga kamfanonin da suka dace su yi wannan dakon na danyen mai.

"An soma bin tsari a bayyane babu rufa-rufa domin samun kamfanonin da za su yi dakon danyen man a jiragen ruwa zuwa matatun mai na Fatakwal da Warri da kuma Kaduna har zuwa lokacin da za a kamalla gyaran bututan mai," in ji Alegbe.

Tun da aka nada Mista Emmanuel Kachukwu a matsayin sabon shugaban NNPC ya sha alwashin tabbatar da tsari ba tare da son zuciya ba kamar yadda shugaba Buhari ya umurce shi.