Ana tunawa da bala'in Hurricane Katrina a Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya gabatar da jawabi na cika shekaru 10 da aukuwar bala'in ambaliyar ruwa da iska mai karfi na Hurricane Katrina wadda ta haddasa barna mai yawa a New Orleans.

Mista Obama ya jinjina wa jama'ar New Orleans bisa yadda suka tunkari iftila'in.

Sai dai ya ce bala'in wanda iko ne na Allah, daga baya ya zamo wani abu da sakaci ya shiga ciki, yayin da gwamnati ta kasa taimakawa jama'arta.

Shugaba Obama ya ce an farfado da al'umomin da bala'in ya shafa ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma mutanen gari.

Ya ce wannan ne birnin da a sannu a hankali kuma da hadin gwiwa yake samun cigaba saboda aikin sake gina shi da keyi ba wai kawai dan a farfado da shi bane ana sake gina shi ne a matsayin sa na birni.

Ya ce an samu ci gaba sosai ta fuskar rage rashin daidaiton matsayi a tsakanin al'ummomin New Orleans.

Fiye da mutane 1800 ne suka mutu a ambaliyar da ta zama bala'i makamancinta mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan 1928, wadda kuma ta haddasa barna a yankunan dake kusa da ruwa a Florida da Texas.