Tarzoma a Yemen: Ko wani hali mutane garin ke ciki?

Hakkin mallakar hoto EPA

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun shafe watanni su na gargadin cewa mutanen kasar Yemen na cikin matsanancin hali, amma ta yaya yanayin rayuwar ta su ta munana?

'Alummar Yemen na fuskantar bala'i a rayuwarsu'.

Wanna ita ce kalmar jami'in da ke gudanar da harkokin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya, Johannes Van Der Klaauw inda ya fede biri har wutsiya a ranar 19 ga watan Agusta.

Tun da lamarin ya munanan tsakanin dakarun da ke goyon bayan shugaban kasar da ke neman mafaka a kasashen waje, watau Abdurabbuh Mansour Hadi da kuma masu goyon bayan mayakan Houthi, an hallaka kusan mutane 4,500, kuma akalla mutane 23,000 ne suka samu rauni a watan Maris.

An rushe gine-gine masu muhimmanci, kuma masu hadin gwiwa da ke kai wa mayakan Houthi farmaki da kasar Saudiyya ke jagoranta, sun saka takunkumi wajen shigowa da kaya kasar, inda ya hana mutane miliyan 21 samun abubuwan more rayuwa.

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Yara fiye da rabin miliyan daya da rabi na fama da yunwa a Yemen.

Yemen ta kwashe shekaru da dama tana fama da rashin kwanciyar hankali da mulkin kama karya da kuma talauci.

'Zaman kashe wando'

Kafin watan Maris din da ya gabata, kusan rabin mutanen Yemen suna fama da talauci da rashin ingantaccen kayayyakin more rayuwa, inda kashi biyu cikin uku na matasan kasar ba su da aikin yi.

A watan Yuni ne Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wata gidauniya domin neman fam biliyan daya na asusun da zai taimakawa mutane kusan miliyan 12.

Amma har a ranar 19 ga watan Agusta, kashi 18 cikin 100 aka samu na kudin, inda dole ta sa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka aro dala 160 daga asusun ta domin dakile tarzomar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hadin gwiwar yaki da ta'adanci da Sudiyya ke jagoranta, ta kafa takunkumin hana shigowa da kayayyaki cikin kasar.

Kasar Saudiyya ta yi alkawarin ba da gudunmuwa ta kudi a lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar neman taimaka, amma har yanzu ba ta cika alkawari ba.