Akbishop da ake zargi da lalata ya mutu

Wani tsohon Akbishop dan asalin Poland wanda ya kamata ya gurfana a kotun babban cocin Vatican bisa zargin yin lalata da yara ya mutu.

Jozef Wesolowski ya fara rashin lafiya ne a watan jiya, sa'o'i kadan kafin ya gurfana a gaban kotun.

Ana zargin sa ne da biyan yara kudi domin yin lalata da su lokacin da yake jakadan Vatican a kasar Dominican Republic.

Tuni kotun na Ikilisiya ta same shi da laifin a farkon wannan shekara, inda ta tsige shi daga matsayin sa.

Ana ganin wannan a matsayin hukunci na farko da za a zartar ga wani babban limanin cocin game da yin lalata da yara a gaban kotu.