An yi harbe-harbe tsakanin Indiya da Pakistan

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption An yi harbe-harbe tsakanin sojojin Indiya da Pakistan.

Jami'an a kasashen India da Pakistan sun ce an yi harbe-harbe tsakanin sojojinsu a kan iyakar kasashen, inda akalla fararen hula 10 suka rasa rayukansu.

An kashe fararen hula shida a yankin Punjab da ke Pakistan yayin da hudu kuma suka mutu a yankin Kashmir na India.

Wannan lamari ya biyo bayan bikin da India ta yi na makwanni uku domin murnar shekara 50 da kasar ta yi na samun galaba a kan Pakistan a shekarar 1965, inda sama da mutane 8,000 suka rasu kuma daukacin su 'yan Pakistan ne.

Yawancin Indiyawa sun goyi bayan shawarar da Firayi ministan kasar Narendra Modi ya dauka ta yin wannan biki, duk da cewa wasu sun soke shi.

Yakin da aka yi a shekarar 1965, yana daya cikin yake-yake hudu da aka yi tsakanin Indiya da Pakistan, tun bayan Biritaniya ta 'yanta su.