Boko Haram: za a bude cibiyoyin ba da umarnin soji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin ta bukaci 'yan Najeriya su taimaka mata da bayanai a kan Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za a bude cibiyoyin bayar da umarnin soji guda biyu -- daya a Najeriya, daya a Kamaru -- a yunkurin da kasashen ke yi na murkushe kungiyar Boko Haram.

Kakakin hedikwatar tsaro ta kasar, Kanar Rabe Abubakar, ya shaida wa BBC cewa za a dauki matakin ne domin bai wa sojojin kasashen damar kai wa 'yan kungiyar hari ta kowanne gefe.

Ya ce, "Muna kokarin bude cibiyoyin bayar da umarni na soji a Najeriya da Kamaru domin mu fahimci juna, sannan hakan zai ba mu ikon shiga kasashen juna domin mu samu galaba a kan 'yan Boko Haram."

Kanar Abubakar ya bukaci 'yan Najeriya su sanya idanu sosai kan abubuwan da ke wakana a kewayensu domin hana ci gaba da aukuwar hare-haren 'yan ta'adda.

Ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya su taimaka wa rundunonin sojin kasar da dukkanin bayanai a kan masu aikata ta'addanci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kawar da 'yan ta'adda.