An zartar da hukuncin kisa kan yan Boko Haram

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Hukumomin kasar Chadi sun aiwatar da hukuncin kisa akan 'yan kungiyar Boko Haram din nan goma da aka yankewa hukun kisa ranar Juma'a.

Wata kotu ce a birnin N'Djamena ta samu yan kungiyar ta Boko Haram da laifi, bayan wasu jerin hare hare da aka kai a birnin wadanda suka yi sanadiyar hallaka mutane da dama.

An dai zartar da hukincin kisan ne da misalin karfe sha daya na safiyar asabar.

Ministan tsaron cikin gida na kasar ta Chadi ne ya shaidawa manema labarai.

Wani mazaunin birnin ya ce an zartar da hukuncin kisan ne a wani babban dandali da ke birnin na N'Djamena, kuma mutane da dama sun hallara domin shaida al'amarin.