Masar:Kotu ta daure yan jaridar Al Jazeera

'Yan jaridar Al Jazeera da kotun Masar ta daure Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan jaridar Al Jazeera da kotun Masar ta daure

An sami Muhammad Fahmy, da Peter Greste da kuma Baher Muhammad da laifi yada rahotannin da ba daidai ba, wanda kuma kotun ta ce zai iya yi wa kasar ta Masar illa.

Lauyar Muhammad Fahmi, daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Amal Clooney, ta bayyana rashin jin dadi akan hukuncin

Daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Peter Greste na Aljazeera, kuma tsohon ma'aikacin BBC, ya bayyana kaduwarsa da hukuncin

Ita ma kafar watsa labaran ta Aljazeera ta ce hukuncin ya saba hankali.