Boko Haram: Sojoji sun gano gidan kera bam

Image caption Wasu daga cikin kayan kera bam na Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram inda suka lalata wani gida da ake kera bam.

Kakakin rundunar Kanar Usman Sani Kukasheka a cikin wata sanarwa ya ce an gano gidan ne a kauyukan Miyati da Nyaleri a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Ya ce sojoji sun kuma kama 'yan kungiyar ta Boko Haram guda uku, ciki har wani shugaban su.

Cikin kayayyakin da sojojin suka gano sun hada da mota da buhunan hatsi da sunduki na yin bom da sauran su.

Dakarun sojin Najeriyar sun kuma danna wasu yankuna na Gambory Ngala domin kwato yankunan da suke hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.