Hari ta sama ya hallaka mutane 31 a Yemen

Hare-haren soji a kasar Yemen Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hare-haren soji a kasar Yemen

Rahotanni daga Yemen sun ce jiragen yakin kawancen da kasar Saudiyya ke jagoranta sun kashe mutane talatin da daya a wani hari ta sama.

Sun kai harin kan wata masana'antar yin kwalaba a arewacin kasar.

Yawancin wadanda suka rasun fararen hula ne.

Kawancen hadakar suna farautar yan tawayen Shi'a ne da aka fi sani da yan Houthi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kusan dubu hudu da dari biyar ne suka rasu, tun bayan da dakarun kawancen suka kaddamar da farmaki a watan Maris.

Ta kuma ce ana fama da tagayyarar al'umma a Yemen.