Austria na bincike kan 'yan ci rani

Kan iyakar kasar Austria
Image caption Kan iyakar kasar Austria

Kasar Austria ta tsaurara binciken ababan bawa a kan iyakokinta dake gabashin kasar, inda ake bi wajen don hana fasakwaurin yan ci rani.

Hakan na zuwa ne bayan da aka gano matattun yan cirani 71 a cikin wata babbar mota da aka yasar a bakin hanya a makon jiya

Yansanda na ta cafke masu fasakwaurin yan ciranin.

Sun ce sun gano yan ci rani fiye da 200 tun a daren jiya, kuma suna tsare da wasu da dama da suke zargi da yin fasakwaurin mutanen.

Hakan dai ya haddasa cunkoson ababan hawa a kan iyakar.

Amma kuma yansanda sun ce binciken na taimakawa wajen ceton rayuka.

Sun ce suna kokarin hana yawan mutuwar yan ci ranin a kan hanyarsu ta ketarawa Turai.