'Boko Haram ta watsu zuwa Lagos'

Hakkin mallakar hoto Nigeria Govt
Image caption Shugaban Najeriya ya bai wa jami'an tsaro wa'adin watanni uku su kawo karshen Boko Haram.

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce kungiyar Boko Haram ta watsu zuwa birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

A wata sanarwa da ta fitar, DSS ta ce ta kama 'yan kungiyar guda 12 a jihar ta Legas tun daga watan Yuli.

Babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan ikirari na DSS.

DSS ta ce ta kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram da kuma wasu 'yan kungiyar da dama a sassa daban-daban na kasar.

Hukumar ta ce ta yi kamen ne a ci gaba da matakan da take dauka na dakile hare-haren mayakan kungiyar.

Hukumar DSS ta ce matsin lambar da 'yan Boko Haram ke fuskanta a arewa maso gabashin kasar inda suke da karfi ne ya sa suka sauya salon kai hare-haren su a yanzu.

Hukumar ta DSS ta ce ta yi kamen ne a jihohin Legas da Kano da Filato da Enugu da kuma Gombe a cikin watan Agusta.

Hukumar ta bukaci jama'a da su rika taimakawa da bayanai game da take taken bata-gari.