Buhari ya lashi takobin kawar da Polio

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya lashi takobin kawar da Polio daga Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin tabbatar da cewar kasarsa ta fita daga jerin kasashen da ke da cutar shan inna a duniya nan da shekara ta 2017.

Shugaba Buhari ya sha wannan alwashin ne a yayin wata ganawa da yayi da gwamnonin jihohin kasar da suka fi fuskantar barazanar cutar shan inna, da jami'an hukumar lafiya ta duniya WHO da na hukumar kiwon lafiya a matakin farko ta kasar a fadarsa.

A watan Yuli dai ne Kasar ta cika shekara daya ba tare da samun ko yaro daya ya kamu da kwayar cutar ba, amma tana bukatar ta kai shekara ta 2017 ba tare da samun cutar ba, kafin hukumar lafiya ta duniya ta cire sunanta daga jerin kasashen da ke da cutar.

A baya dai Najeriya ta kasa cimma nasarar yaki da cutar shan innar sanadiyyar matsalolin da suka hada da kyamar allurar rigakafi da rashin kai wa ga yaran da ke kauyuka masu nisa, tare da matsalar sanya addini da siyasa a batun yaki da cutar shan innar.