Buhari ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnati

Image caption Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati da Shugaba Buhari ya rantsar.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir David Lawal, da sauran manyan jami'an da ya nada.

Sauran mutanen da ya rantsar su ne: Alhaji Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa; Kanar Hameed Ali (mai ritaya) a matsayin shugaban hukumar hana fasa-kauri; Mista Kure Abeshi, a matsayin shugaban hukumar shige-da-fice.

Kazalika, Shugaba Buhari ya rantsar da Manjo Janar Babagana Mungono (Mai ritaya) sabon mai ba shugaban shawara kan sha'anin tsaro da kuma Mr. Femi Adesina, mai ba shugaban kasar shawara kan watsa labarai

Sauran su ne: Sanata Ita S. Enang, a matsayin mai ba shi shawara a kan harkokin majalisar dattawa; Alhaji Suleiman A. Kawu, a matsayin mai ba shi shawara a kan harkokin majaliasar wakilai.

Shugaba Buhari ya bukace su da su yi aiki tukuru domin ci gaban kasar.

A nasa jawabin, sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, ya ce Allah ne ya cusawa Shugaba Buhari hikimar nada shi da sauran wadanda ya nada kan mukamansu ba tare da la'akari da kabila ba.

Ga alama dai yana mayar da martani ne ga korafe-korafen da suka biyo bayan nadin nasu na cewa shugaban ya nuna son kai ga yankinsa na arewa.