Ladani ya sauya yadda ake kiran Sallah a Masar

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu musulmai ne suka kai karar ladanin.

Wani ladani a kasar Masar yana fuskantar hukunci bayan da ya sauya yadda ake yin kiran Sallah.

Ma'aikatar da ke kula da addini ta kasar ta ce za ta dauki matakin shari'a a kan ladanin, Mahmoud al-Moghazi, wanda mai makon ya ce Assalatu Khairun minan-naum, wato dadin Sallah ya fi dadin bacci; sai ya ce rika cewa Assalatu Khairun minan-Facebook, wato dadin Sallah ya fi yin Facebook.

Wasu musulmai ne dai suka kai karar sa bisa zargin sauya kalaman da ake yin kiran Sallah.

Mahmoud al-Moghazi ya shaida wa wani gidan talabijin cewa zai fara "yajin cin abinci", yana mai yin roko ga Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar da ya tsoma baki a cikin lamarin.

An dakatar da Mr Moghazi daga yin kiran Sallah har sai an gama bincike a kan lamarin.