Facebook zai hana amfani da bidiyon sata

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Mark Zuckerberg shi ne wanda ya kirkiri shafin Facebook.

Shafin sada zumunta na Facebook ya ce zai fara amfani da wata sabuwar fasaha domin dakatar da mutane sanya bidiyo ba tare da izini ba.

Masu shirya fina-finai sun yi korafin cewa shafin sada zumuntar ba ya irin kokarin da ya kamata wajen dakatar da mutane amfani da bidiyon da ba nasu ba ko kuma wasu bangarorin bidiyon ta inda suke sanya su a matsayin mallakin su.

Sabon tsarin ba zai dinga kawar da bidiyon da aka sata ba, amma zai ankarar da mai bidiyon cewa an sake amfani dashi.

Wasu mutane kalilan ne za su fara amfani da sabuwar fasahar a matsayin gwaji.

A watan Ogusta, wani shahararre a shafin bidiyo na YouTube Hank Green ya soki kamfanin saboda jan kafa da yake yi na daukar mataki game da satar fasahar bidiyo.