Ghana na zaben kananan hukumomi

Hakkin mallakar hoto Chris Stein AFP
Image caption Jami'an tsaro sama da dubu arba'in ne za su tabbatar da tsaro a lokutan zaben.

A ranar Talata ne al'ummar kasar Ghana ke zaben 'yan majalisun kananan hukumomi da bai da nasaba da siyasa.

Hukumomin kasar sun ce an samar da Jami'an tsaro sama da dubu arba'in don tabbatar da tsaro a sassa daban daban na kasar.

Kimanin 'yan takara dubu goma sha takwas ne da suka hada da maza da mata suka tsaya takara don neman mukamai daban daban a kasar.

Za'a bude rumfunan zabe ne daga karfe bakwai na safe zuwa karfe biyar na maraice.