'Yan fim za su gana a kan matsalolin Kannywood

Image caption Ana zargin hukumar tace fina finai da rashin yin aikinta yadda ya kamata.

Daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fina finan Hausa za su gana da hukumar tace fina finan jihar Kano da ke Najeriya.

Bangarorin biyu za su yi taron ne ranar Jumma'a a ofishin hukumar da zummar lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka addabi masu yin fim din da aka fi sani da Kannywood.

Wata sanarwa ta ce ana gayyatar daraktoci daga Kano da Kaduna da Jos da Katsina da Sokoto da Abuja domin su halarci taron.

Ana zargin 'yan fim din da yin fina finan da ke gurbata tarbiya, koda yake sun sha musanta zargin.

Ita ma hukumar tace fina finan, ana zargin ta da rashin gudanar da aikinta yadda ya kamata; shi ya sa ma, a cewar masana, ake samun fina finan da ba su da kan-gado.

Kazalika, masu sana'ar ta fim na kokawa da ayyukan masu satar fasaha.