Ana ci gaba da zanga zanga a Malaysia

Mr Najib  ya ce zanga zanga ba ita ce hanyar bayyana ra'ayoyi ba a tsarin mulkin demukradiyya.
Bayanan hoto,

Mr Najib ya ce zanga zanga ba ita ce hanyar bayyana ra'ayoyi ba a tsarin mulkin demukradiyya.

Firayiministan kasar Malaysia Najib Razak ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake masa akan ya sauka daga kan mukamin sa saboda badakalar cin hanci da rashawa.

Dubban mutane ne dai suka shiga cikin masu zanga-zanga akan titunan kasar a karshen mako, inda suka bukace shi da ya yi murabus saboda zargin sa da wawure miliyoyin daloli na kasar.

Sai dai Mr Najib a wani jawabi don tunawa da zagoyar wa ranar samun 'yancin kan kasar ya musanta zarge zargen.

Firayiministan ya yi kuma alla-wadai da zanga zangar da ya ce ba ita ce hanyar data dace ba na bayyana ra'ayoyi a tsarin mulkin demukradiyya.