Kungiyar Boko Haram ta watsu zuwa Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce kungiyar Boko Haram tana kokarin fadada ayyukanta zuwa wasu jihohin kasar wanda ya hada da jihar Lagos, inda nan ce babbar cibiyar kasuwancin kasar.

Hukumar lekan asiri ta Najeriya DSS ta ce ta kame 'yan kungiyar Boko Haram 12 a jihar Lagos tun a watan Yuli.

Babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan ikirari na DSS.

Boko Haram ta shafe shekaru shida tana kai hare-hare arewa maso gabashin kasar.

"Karin Bayani"

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta kara da cewa ta kama wasu wadanda suka bayyana kansu a matsayin 'yan kungiyar Boko Haram a jihar Enugu da ke Kudu maso gabashin kasar har ma da wasu sassa da ke tsakiya da arewacin Najeriyar.

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, ta danganta kokarin kungiyar Boko Haram na fadada ayyukanta zuwa yankunan da ke kudancin Najeriya da matsin lambar da kungiyar ke funskanta a arewa maso gabashin kasar inda suke da karfi.

Rahotanni sun ce an kashe sama da mutane 50 a wani hari da kungiyar ta kai Jihar Borno a ranar Juma'a, sai dai kuma wakilin BBC Will Ross wanda ke jihar Lagos ya ce har yanzu 'yan Boko Haram suna haddasa hatsaniya a arewa maso gabashin Najeriya.

Wakilin BBC ya ce mazauna jihar Lagos da dama zasu tsorata idan suka ji cewar an kama 'yan Boko Haram da dama a makonnin baya-bayan nan.

Ya kara da cewar 'yan jihar da dama sun sha shaida masa cewa mayakan Boko Haram ba za su taba gangancin kai hari Lagos ba, sai ga hasashen su na neman rushewa, musamman ma lokacin da aka yi kokarin kai harin bam a wata cibiyar rarraba mai ta jihar a bara.

Hukumar DSS ta fitar da sanarwar ne kwana guda bayan wata sanarwa mai tayar da hankali wacce ta ce an kama wani matashi a filin jirgin sama da ke Abuja a lokacin da yake kokarin tattara bayanan sirri ga Boko Haram.

Hukumar ta ce kamen kwamandojin Boko Haram da kuma wasu 'yan kungiyar ya taimaka wajen hana munanan hare-hare.

DSS ta kara da cewa hakan ya taimaka wajen kare afkuwar kawo wasu hare-hare masu muni.

A watan Yuli ne aka nada sabon Darakta Janar na hukumar DSS kuma bayanan baya-bayanan sun ce an fara kamen ne a makon farko bayan an nada shi.

Boko Haram a Takaice:

Hakkin mallakar hoto AFP

* An kafa kungiyar a shekarar 2002, da farko sun kyamaci karatun Boko. Boko Haram na nufin an haramta makarantar Boko.

*Ta kaddamar da hare-hare masu yawa a shekarar 2009.

* An kashe dubban mutane a arewa maso gabashin Najeriya kuma sun yi garkuwa da daruruwan mutane da suka hada da 'yan matan makarantar Chibok 200.

*Kungiyar ta yi mubaya'a ga kungiyar IS, wacce yanzu ta ke kiran kanta kungiyar kafa daular musulunci a Afrika ta yamma.

*Sun kwace yankuna da dama a arewa maso gabas, inda suke kokarin kafa daular musulunci.

*Sojojin hadin gwiwa na yankin tafkin Chadi sun kwato garuruwa da dama daga 'yan kungiyar Boko Haram a wannan shekarar.